Uwargidan tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ta nuna goyon bayanta kan salon tafiyar da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Patient Jonathan wadda ta kasance matar tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ta ce ba za ta koma fadar shugaban ƙasa ba za ta ci gaba da taya uwargidan shugaban kasa Oluremi Tinubu yaƙin neman zaɓe.

Ta bayyana haka ne a Abuja jiya Asabar yayin da aka karramata a matsayin mace jagira kuma abin koyi a shekarar 2025.

Ta ce ta na goyon bayan tsarin karɓa-karɓa a mulkin ƙasar domin samar da haɗin kai.

A cewarta, ba ta da niyyar komawa fadar shugaban ƙasa kuma za ta ci gaba da mara baya kan tafiyar da salon mukin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ta ce a lokacin da ya kasance ba kai ke jan ragamar ƙasa ba, to kyautuwa ya yi mutum ya koma gefe yadda za a samu cigaba a ƙasar.

Patient Jonathan ta ce ba iya sanayya ce kaɗai a tsakaninsu da mai dakon shugaba Bola Ahmed Tinubu ba sun yi aiki tare kuma ta san wacece ita.

Ta ce jaddada goyon bayanta ga shugaba Tinubu da kuma mai dakinsa wana ta musanta dukkan raderadin da ake yi kan siyasa a tsakaninsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: