Wasu rahotanni sun bayyana cewa Mayakan boko-haram a Jihar Borno sun sake kai’wa sansanin soji na Karamar hukumar Marte hari, tare da hallaka sojojin da ba a kai ga gano adadinsu ba.

Majiyoyin daga yankin sun ce lamarin ya faru ne a sansanin Forward Operation Base na Bataliya ta 153 Task Force da misalin ƙarfe 3:00 na daren yau Litinin.
Guda daga cikin majiyoyin da ya nemi da a sakaya sunansa, ya ce ‘yan ta’addan sun kuma kama wasu daga cikin sojin, daga bisani suka kwashe makamai, harsasa, tare da kone motocin yaki.

Acewar Majiyar ‘yan ta’addan sun kwashe ikon Karamar hukumar ta Marte, inda kuma da dama daga cikin sojojin suka tsere zuwa Dikwa, a runduna ta 24 da ke garin na Dikwa.

Karamar hukumar ta Marte na da tazarar kilomita 38 daga Dikwa, hedkwatar ƙaramar hukumar Dikwa a jihar.
Sai dai wata majiya daga Dikwa ta ce an jiyo karar harbe-harbe, inda jirgin yaƙin rundunar sojojin saman ya yi shawagi a yankin.
