Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Kasa NDLEA ta kama wata mata da take kokarin yin safarar miyagun kwayoyi zuwa Kasar Iran.

Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi.
Kakakin ya ce matar mai suna Miracle Obehi, ta boye miyagun kwayoyin ne a cikin al’aurarta, da kuma jakarta daga bisani kuma ta sanya hijabi.

Acewar Babafemi matar na shirin shiga jirgin Qatar Airline zuwa Doha, ne a filin sauka da tashin jiragen sama na garin Fatakwal.

Femi ya ce Matar ta hadiye kwayoyi 67 a cikinta, yayin da ta boye wasu a cikin jakarta, daga bisani kuma ta boye wasu a cikin al’aurarta.
Kazalika ya ce hukumar ta tilasta mata fitar da wadanda ta hadiye, inda ta ce an shirya cewa za ta hadiye kwayoyi 70, daga bisani kuma ta gaza karasa shanye ragowar, inda ta saka a cikin al’aurarta ta.