Shugaban kamfanin mai na Najeriya NNPCL Bashir Bayo Ojulari ya ce za su ci gaba da aikin haƙo mai a yankin arewacin Najeriya.

Ojulari ya bayyana haka ne a yayin wata tattaunawa da aka yi da shi cikin harshen Hausa da gidan jaridar BBC ta yi da shi.


Ya ce a halin yanzu farashin mai ya faɗi a kasuwar duniya kuma sauƙin zai gangaro zuwa masu soya don amfani da shi.
Dangane da tsamin dangantaka tsakanin kamfanin da matatar mai ta Dangote, ya ce za su tabbatar sun ɗinke ɓarakar ba tare da ta sake faruwa ba.
Ojulari ya bayyana cewar a halin yanzu su na iya ƙoƙarinsu don rage kuɗaɗen da su ke kashewaa kamfanin don bai wa Najeriya damar amfani da kuɗaɗen da za ta samu daga kamfanin don yi wa ƙasa aiki da au.
Daga karshe ya bukaci goyon bayan ƴan ƙasar musamman arewa don ganin an samu nasarar da za ta ciyar da ƙasar gaba.