Kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya da sarakunan gargajiya sun jaddada goyon bayansu kan samar da ƴan sandan jihohi.

Aikin da ke gaban majalisa bayan da jihohin Najeriya su ka miƙa bayanin matsayarsu a kai.

A wani taro da ƙungiyar ta yi a Kaduna, sun buƙaci majalisa a ƙasar da ta ci gaba da aikin bai wa jihohin damar kafa yan sandan su.

Taron wanda aka yi a gidan Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna jiya Asabar, ya samu halartar sarakunan gargajiya da gwamnonin arewa

A wata sanarwar hadin gwiwa da su ka fitar dauke da sa hannun shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya, sun ce sun tattauna yadda za su haɗa kai da gwamnonin Najeriya don tallafawa gwamnatin tarayya ta fuskar tsaro.

Daga cikin matakan da su ke gani za a shawo kan matsalar tsaron idan an ɗauka akwai batun bai wa jihohi damar ƙirƙirar ƴan sandansu.

Gwamnonin sun jaddada bukatar hadin gwiwa domin dakile cigaba da fuskantar matsalar tsaro a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: