Gwamnan Jihar Kaduna Malam Uba Sani ya bayyana takaicinsa kan yadda matasan yankin Arewa Maso Yammacin Kasar nan suka rungumi dabi’ar ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Malam Uba Sani ya ce matasa na shan magunguna irin Tramado, Codeinel ba bisa ka’ida ba, da kuma miyagun kwayoyi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a gurin wani taro da kungiyar masana harkar magani,
Pharmaceutical Society of Nigeria, ta Jihar Kaduna ta shirya.

Gwamnan wanda ya samu wakilin shugaban hukumar wayar da kan mutane illar shan miyagun kwayoyi na Jihar Joseph O. Ike, ya ce shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasa ya ta’azzara.

Acewarsa mtum ɗaya cikin mutane biyar daga cikin masu amfani da irin magunguna na faɗawa cikin dogon shaye-shaye, wanda akan ke haifar da barazana ga al’umm, harma da tsaro da ci gaban yankin.

Gwamnan ya kuma tabbatar da aniyarsa ta yin haɗin gwiwar tsakanin gwamnatinsa da masana harkar magani, wanda hakan zai ƙara ƙarfi don shawo ci gaba mai ɗorewa a fannin kiwon lafiya a jihar Kaduna da Kasa baki ɗaya.

Kungiyar ta gudanar da taron ne domin taya murna ga sabon shugabab kungiyar na Kasa Pharm Ayuba Ibrahim da mataimakiyarsa a ynkin Arewa Pharm Aisha Isyaku.

Leave a Reply

%d bloggers like this: