Rundunar sojin Najeriya ta kama wasu mutane da ake zargi na kai wa ƴan bindiga makamai.

 

Jami’an karkashin Operation Safe Haven ne su ka kama mutane biyun da ake zargi su na kai wa masu garkuwa da mutane makamai.

 

An kama mutanen a ƙaramar hukumar Barikin Kadi ta jihar Filato.

 

Mutanen sun haɗa da Yahaya Adamu da Saeedu Haruna an kamasu bayan samun bayanan sirri a kansu

 

Mai magana da yawun dakarun Major Nantip Zhakom ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi cewar, an kama Adamu a ranar 10 ga watan Mayu da mu ke ciki a Barakin Gangare.

 

Kama Adamu ne ya bayar da damar kama abokin huldarsa a ranar 11 ga watan Mayu a Marit Mazat sa ke Barikin Kadi.

 

A wajen Haruna an samu bindiga kirar AK47 guda saya da harsashi da wayar hannu

 

A binciken da su ka fara yi sun gano mutanen na taimakawa wajen muggan ayyuka da ake yi a jihar, da kuma yankin ƙaramar hukumar Sanga a jihar Kaduna

Leave a Reply

%d bloggers like this: