Wasu ‘yan bindiga sanye da kayan jami’an ‘yan sanda sun kai wani hari wata makarantar Sakandiren gwamnati da ke Raka cikin karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, inda suka hallaka wani Malami mai suna Mallam Kabiru Abdullahi, tare da yin garkuwa da wasu mata uku ciki harda matar malamin.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, da misalin karfe 8:00 na dare.

Guda daga cikin jami’an gudanarwa na Makarantar, ya ce ‘yan bindigar sun shiga Makarantar ne ta cikin wata Kofa da ke bayan Katangar Makarantar, sannaan suka kuma tsere ta nan.

Acewarsa Maharan sun zagaye makarantar ne sanye da kayan na ‘yan sanda, hula, da kuma Takalmin roba.

Sai dai rahotanni sun bayyanna cewa Maharan sun hallaka malamin ne a lokacin da yayi musu gaddama wajen tafiya dashi, daga bisani kuma suka tsere tare da matan.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Jihar Yazid Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce maharan sun shiga makarantar ne bayan sun fasa katangar.

Kakakin ya ce a halin yanzu jami’an na kokarin ganin sun kubtar da wadanda aka sace tare da kuma da tabbata da tsaro a yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: