Ministan birnin tarayya Abuja Nysom Wike ya ce jam’iyyar PDP ba za ta taɓa samun nasara a babban zaben shekarar 2027 da ke tafe ba.

Wike ya ce son kai da kuma nuna buƙata ne ya sa jam’iyyar ke rugujewa wanda zai hanata samun nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2027.
Ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai da ya yi a Abuja.

Ya ce shugabanci ne kashin bayan cigaba ko akasinsa.

Dangane da batun ficewar gwamnan jihar Delta da mukarrabansa zuwa jam’iyyar APC, ya yi tambaya kan cewar hakan laifi ne? Ko kuwa goyon bayan shugaba Tinubu ne laifi?
Wike ya yi ikirarin cewar shi kadai ne tsohon gwamnan da bai goyo bayan shugaban ƙasa ba amma ya tabbatar da jam’iyyarsu ta PDP a jiharsa ta samu nasara a kowanne mataki.
Ministan ya yi gargadi kan gaza magance rikicin cikin gida da ya ƙi ci y ƙi cinyewa a cikin jam’iyyar wanda ya ci zai ci gaba da ruruwa ne matukar ba a dauki mataki ba.
