Hukumar kula da yanayi ta Kasa NIMET ta bayyana cewa Jihohi Shida daga cikin Jihohin Kasar nan za su fi kowacce Jiha fuskantar yawan samun ruwa.

Jihohin sun hada da Bayelsa, Legas, Akwa-Ibom, Rivers, Cross River, da kuma Delta.
Acewar hukumar Jihohin za su samun ruwan ne tsawon kwanaki 250 zuwa 290, kamar yadda hukumar ta bayyana a sanarwar da ta fitar jiya Litinin, kan ruwan da za a samu a wannan shekarar ta 2025.

NiMet Jihohin da za su biye musu baya kuma su ne Ogun, Oyo, Ekiti, Osun, Ebonyi, Anambra, da kuma Enugu, inda za su samu ruwan tsakanin kwanaki 200 zuwa 250.

Hukumar ta ce a Jihohin Nasarawa, Neja, Kogi, Benue, Filato, Kwara, da kuma Abuja za su samu ruwa na tsakanin kwanaki 150 zuwa 200.
NIMET ta kara da cewa a Jihohin Kano, Jigawa, Katsina, Sokoto, Zamfara, Borno, Yobe, kuma za a samu ruwa na kwanaki 110 zuwa 150.