Jam’iyya mai mulki ta APC ta bayyana cewa ko kadan ba ta da niyar mayar da Najeriya tsarin jam’iyya daya.

Sakataren yada labaran Jam’iyyar Felix Morka ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa.

Felix ya kara da cewa duk da yawaitar samu masu sauya shekar da ake yi daga wata Jam’iyyar zuwa APC, hakan ba zai sanya ta mayar da Kasar tsarin jam’iyyar guda ba.

Acewarsa a lokacin da Jam’iyyar PDP, ke mulki a Naajeriya ta rike sama da jihohi 28 ba, amma ko kadan ba a zarge ta da wani ƙoƙarin na mayar da ƙasar mai tsarin jam’iyya ɗaya ba.

Sakataren ya ce babu wani laifi ga mambobin jam’iyyun PDP da LP da suke sauya sheka zuwa APC.

Leave a Reply

%d bloggers like this: