Ministan Birnin Tarayya Abuja Nyesom Wike ya musanta rahotonnin da ake yadawa cewa yana shirin tsayawa takarar shugaban Ƙasa a zaben sekarar 2027 da ke tafe.

Wike ya musanta rahoton ne a yayin ganawarsa da manema labarai a yau Asabar a Abuja.
Ministan ya bayyana takaicinsa kan jita-jitar, inda ya bayyana cewa bashi da sha’awar tsayawa takarar shugaban Ƙasa, don kuma yin takara da shugaban Ƙasa Bola Tinubu.

Ministan ya ce ko kadan ba zai iya yin takara da shugaba Tinubu ba, yana mai bayyana hakan a matsayin cin amana, duba da yadda yake aiki a karkashin gwamnatinsa.

A yayin tambayar da aka yiwa Wike, kan cewa zai tsaya takarar idan jam’iyyarsa ta PDP ta bashi dama, Wike ya yi watsi da lamarin, yana mai cewa ba zai fara daukar matakin hakan ba.
Bugu da kari Wike ya ce babu wata Jam’iyyar adawa da ta isa ta Kifar da gwamnatin shugaba Tinubu a zaben 2027 da ke tafe.