Gwamnatin Jihar Kano ta hannun hukumar tace fina-finai ta jihar ta haramta bikin Ƙauyawa a lokacin bukukuwa da ake gudanarwa, a kokarin hukumar na tabbatar da kauda aikata baɗala a Jihar.

Shugaban hukumar Abba El-Mustapha ne ya tabbatar da hakan a yau Asabar a yayin taron ‘yan Jaridu a Jihar.

Shugaban ya kara da cewa hukumar ta kuma dakatar da dukkan guraren da ake gudanar da bukukuwan har uwa lokacin da hali ya yi.

Acewar shugaban mataki wani yunkuri ne daga hukumar na tabbatar da tarbiyya, tabbatar da dabi’u masu kyau a tsakanin Al’umma, da kuma kare martabar Al’adu.

Har ila yau ya kara da cewa mataki na daga cikin sabuwar dokar da majalisar dokokin Jihar ta amince dashi, daga bisani kuma gwamnan Jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu akanta.

Bugu da kari ya ce sabuwar dokar ta bai’wa hukumar damar sanya idanu da kuma kura da dukkanin guraren taruka da kuma ayyukan masu DJ a jihar.

El,Mustapha ya ce daga yanzu dukkan wanda aka gani ya shirya wani taro da sunan Kauyawa babu shakka ya aikata kaifi.

Akarshe shugaban hukumar ya nemi hadin kan, hukumar Hisba, jami’an tsaro na ganin cewa an tabbar da matakin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: