Tsohon gawamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP a Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya musanta batun cewa yana shirin shiga haɗakar siyasa da ake shirin yi a Najeriya.

Kwamkwaso ya bayyana hakan ne a yau Asabar ta cikin wata wallafa da ya fitar.

Tsohon gwamnan na Kano ya bayyana lamarin a matsayin makirci na wasu ‘yan siyasa.

Kwankwaso ya ce ko kadan babu ƙanshin gaskiya a cikin rahoton, da ake yadawa, inda ya bukaci mutane da su yi watsi da shi.

Acewar Kwankwaso ta daina cewa uffan akan al’amuran da suka shafi siyasar Najeriya, yana mai cewa zai yi magana ne a lokacin da ya kamata.

Akarshe Kwankwaso ya buƙaci al’ummar Kasar nan da su dinga dogara da hanyoyin sadarwarsa a hukumance, a dukkan lokacin da suke son tabbatar da sahihancin wani abu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: