Jami’an runduna ta 6 da ke garin Jalingo a Jihar Taraba sun samu nasarar hallaka ’yan bindiga biyu tare da ƙwato shanu 1,000 daga hannunsu.

Muƙaddashin Daraktan yaɗa labarai na rundunar sojojin, Kyaftin Oni Olubodunde ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikewa da manema labarai a yau Juma’a a garin Jalingo.

Acewarsa jam’an sun samu nasarar hallaka ‘yan bindigan da kuma ƙwato shanun ya biyo bayan wani bayanan sirri da rundunar ta samu kan shuguban ’yan bindigar akan bubura 30, inda suka nufi wani yanki na Ƙaramar hukumar Karim Lamiɗo domin satar shanun fulani.

Oni ya ce yan ta’addan sun shigo Jihar Taraba ne daga Jihar Filato domin aikata ta’addanci tare da sace shanun, inda suka shiga yankin Jebjeb don shiga wasu rugagen Fulani.

Ya ce bayan samun bayanan sirri sojojin sun kashe ‘yan bindiga biyu daga cikinsu, tare da kokarar sauran, da ƙwato shanu 1,000 wanda ’yan ta’addan suka sace.

A karshe ya ce a halin yanzu sojojin na kan tantace masu shanu domin mayar masu da shanun su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: