Jam’iyyar NNPP ta ƙasa ta tabbatar da cewa tsohon gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya fice daga cikin jam’iyyar tun a watan Yunin 2023 da gabata.

Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dr Agbo Gilbert Major ne ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin ‘Daily Politics’ na Trust TV.

Agbo ya bayyana cewa Kwankwaso ya fice daga NNPP ne tare da mabiyansa.

Kazalika ya ce bisa tsarin Jam’iyyar da kuma hukuncin kotu a Jihar Abia da Abuja, kwankwaso ba ya cikin jam’iyyar tun 2023.

Shugaban ya ce tuni Kwankwaso ya zama tarihi a jam’iyyar NNPP.

Leave a Reply

%d bloggers like this: