Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Elrufai ya ce cin hanci da rashawa ya mamaye alkalai da lauyoyin Najeriya.

Elrufai ya bayyana hakane yau Litinin yayin da ya hakarci taron makon lauyoyi a Abuja.
Ya ce a yanzu mutane ba sa gamsuwa da alkalai saboda hukuncin da su ke yin kan son zuciya.

Ya ce alkalai na yin hukunci don tallafawa masu kuɗi da masu mulki a Najeriya.

Elrufai ya zargi wasu lauyoyi da amfani da kotuna don bukata ta siyasa.
Daga karshe ya yi kira ga kwararrun lauyoyi da Alkalai da su kasance masu tsayawa kan aikinsu tare da kaucewa cin hanci da rashawa.