Rundunar ƴan sanda a jihar Katsina sun kubutar da mutane biyar da aka yi garkuwa da su.

 

Mai magana da yawun yan sanda a jihar Abubakar Sadik Aliyu ne ya baayyana haka jiya Talata.

 

Ya ce an kubutar da mutane wadanda fasinjoji ne a Unguwar Basau da ke hanyar Funtua zuwa Gusau

 

Yankin na ƙarƙashin ƙaramar hukumar Faskari a jihar.

 

A cewarsa lamarim ya faru ranar Litinin da ƙarfe 9:37pm na dare wanda su ka samu kiran wata kan masu garkuwa fa su ka tare hanyar.

 

Da samun kiran ne kuma su ka yi gaggawar hada tawagarsu tare da dakile shirinsu.

 

Ya ce yan bindigan sun tare motoci guda biyu amma sun samu nasarar kubutar da direbobin biyu da fasinjojin uku.

 

Kwamishinan yan sanda a jihar ya yabawa jami’an sa bisa kokarin kubutar da mutanen.

 

Sannan ya buƙacesu dansu ci gaba da jaiircewar wajen yaki da yan ta’addan a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: