Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce jam’iyyar PDP a yanzu na sheshshekar mutuwa shi ya sa jama’ar cikinta ke ficewa zuwa APC.

Ganduje ya bayyana haka ne a taron da aka yi yau a fadar shugaban kasa wanda ya tabbatar da cewar jam’iyyar APC ce za ta sake lashe zabe a zaben da za a yi a Abuja.


Ya ce ganin yadda jam’iyyar APC ke ƙara samun magoya baya ya sa mambobin jam’iyyar PDP ke ficewa su na komawa cikin jam’iyyar APC.
A cewarsa zuwa yanzu su na da gwamnoni 22 cikin jihohi 36 da ke cikin jam’iyyar APC kuma duk da haka akwai karin gwamna guda da ke kan hanya.
Dangane da nasarar da su ka samu a zabukan da aka yi na baya bayan nan, Ganduje ya ce a shirye su ke don don shiga zabe a jihar Anambra da sauran jihohin.
Kuma nasarar da jam’iyyar ta samu a zaɓukan da aka yi bayan babban zaɓen shekarar 2023 alama ce ta abinda zai faru a babban zaɓen shekarar 2027 da ke tafe
