Masu ruwa da tsaki da jagororin jam’iyyar APC a shiyyar arewa ta tsakiya sun nuna goyon bayansu ga shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu don sake zarcewa a karo na biyu.

Jagororin dai sun bayyana haka ne don ganin an dora da ayyukan da shugaban ya faro da farko.


Daga cikin waɗanda su ka halarci taron kawai sakataren gwamnatin tarayya Sanata George Akume da shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Kwara Abdul Rahman Aabdulrazak da gwamnam jihar Nassarawa kums hugaban kungiyar gwamnonin arewa ta tsakiya
Sauran su ne gwamnan jihar Benue da gwamnan jihar Neja da gwamnan jihar Kogi sai shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje.
Haka kuma akwai tsaffin gwamnonin Kogi, Kwara, Nassarawa, Filato, da sauran masu r a da tsaki.
Sannan akwai ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a.
Gamayyar masu ruwa da tsakin sun nuna goyon bayansu ga shugaba Tinubu don ganin ya samu damar sake darewa kujerar shugaban ƙasa a kakar zabe ta shekarar 2027.
