
Masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC a jihar Benue sun nuna goyon bayansu ga shugaba Bola Ahmed Tinubu don sake zarcewa wa’adi na biyu a matsayin shugaban ƙasa.
Daga cikin waɗanda su ka nuna goyon bayan nasu akwai sanatoci biyu da yan majalisar wakilai ta tarayya mutane goma.

Sannan sun yi kira ga gwamnan jihar Hyacinth Alia da ya haɗa kai da gwamnatin tarayya don kawo ƙarshen matsalar tsaro da ake fuskanta a jihar.

Masu ruwa da tsakin sun bayyana haka ne yayin taron manema labarai da su ka yi a majalisar.
Sanatocin dai sun haɗa da Titus Zam da Emmanuel Udende.
Tun a naya ake ta samun masu nuna goyon bayansu ga shugaba Bola Ahmed Tinubu don sake zarcewa wa’adi na biyu a matsayin shugaban ƙasa.
Sai dai har yanzu shugaban bai bayyana kan ra’ayinsa na sake neman kujerar shugaban kasa ba.
