Tsohon gwamnan Jihar Kogi Yahya Bello ya musanta rade-raden cewa yana shirin tsayawa takarar shugaban Ƙasa a zaben 2027 da ke Tafe.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Michael Ohiare ya fitar a yau Juma’a.
Tsohon gwamnan na Kogi ya bayyana cewa mutane na yaɗa wani faifan bidiyo ne wanda lamarin ya faru tu a shekarar 2022 da gabata.

Yahya Bello ya ce mutane na yada tsohon bidiyon ne, da nufin yana yaƙin neman zaɓen takarar shugaban Ƙasa na shekarar 2027 da ke tafe.

Sanarwar ta kara da cewa mutane sun dauko tsohon bidiyon suna yaɗawa ne, domin haifar da rikici tsakaninsa shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
Yahya Bello ya ce shima yana goyan bayan sake komawar shugaban Ƙasa Bola Tinubu wa’adi na biyu na mulkin Ƙasar nan, a don haka ya bukaci mutane da su yi watsi da raɗe-radɗen.