Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya dake komawa garin Marte bayan shafe awanni da daddare ranar Asabar.

Gwamnan ya sake komawa garin jiha Alhamis do tabbatar da komai ya daidaita a bangaren tsaro a yankin.

Tun bayan wasu hare-haren ƴan Boko Haram, daga bisani gwamnan ya kai ziyara Marte, Kala Balge, Wulgo, Ngala, Gujibo, Lugumani, Ajiri, Koibe da Dikwa.

A ziyarar da gwamnan ya kai Marte ya yi wata ganawar sirri da kwamandojin sojojin yankin.

Sannan ya samu rakiyan mambobin yankin a majalisar wakilai da kwamishinoninsa da manyan mukarraban gwamnatinsa.

A kwanakin nan dai an samu karuwar hare-haren yan Boko Haram a jihar Borno wanda gwamnan ya yi zargin cewar yan Boko Haram na shirin kwace garin Marte.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: