Haɗin gwiwar jami’an Operation haɗin Kai da jami’an sojin Sama sun samu nasarar dakile wani yunkurin ƴan ta’addar ISWAP da suka nufi kai’wa garin Damboa da ke Jihar Borno.

Mai sharhi kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi Zagazola Makama ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a.
Zagazola ya bayyana cewa a yayin daƙile harin jami’an sun hallaka ‘yan ta’addan 16, a musayar wutar da suka yi da misalin ƙarfe 1:00 na daren yau Juma’a.

Ƴan ta’addan sun kai hari runduna ta 25 da ke Damboa da kuma kan gadar Azir, inda jami’an suka yi musayar wuta da ‘yan ta’addan ta sama da Ƙasa.

Makama ya ce ƴan ta’adda da dama ne suka jikkata a yayin harin, yayin da 16 suka rasa rayukansu.
Sai dai ya ce a yayin lamarin jami’an soji biyu sun rasa rayukansu.