Gamayyar jami’an tsaron ƴan sanda da na Sa-kai sun kama Hakimin garin Guiwa Garba Mohammed da ke cikin karamar hukumar Mashegu a Jihar Neja bisa zarginsa da tallafawa ƴan bindiga a Jihar.

Jami’an tsaron sun kama shi ne tare da wasu mutane 13 da ake zargi suma na da hannu a cikin lamarin.
An kama waɗanda ake zargin ne a ranar Juma’a da misalin karfe 9:00 na safiya bayan samu bayanan akansu.

Nasarar kama Hakimin da mukarrabansa ta samu ne a samamen hadin gwiwa da jami’an tsaron suka domin kawo karshen ta’addan a yankin Mashegu.

Hakimi na bai’wa ‘yan ta’addan gurin fakewa, a gidansa tare da shirya yadda za su kai hare-hare, yayin da sauran kuma suka fito daga Ƙauyuka daban-daban da ke yankin, inda suma suke tallafawa ƴan ta’addan.
Sannan hadakar Jami’an sun kai samamen sansanonin ƴan bindigar dake kauyukan Guiwa da Telle da ke cikin yankin.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Jihar asiu Abiodun ya tabbatar da kama waɗanda ake zargin.
Kakakin ya ce a ranar 22 ga watan Mayun nan jami’ansu sun kai samame dazukan Magaman-Daji da tare, da kokarar ƴan ta’addan, inda kuma a ranar 23 ga watan Mayun da misalin ƙarfe 9 na safiya, jami’an nasu suka sake shiga ƙauyukan Guiwa da Telle bayan samun bayanai, inda suka kama hakimin Guiwa da sauran mutanen.