Majalisar dokokin Jihar Katsina ta goyi bayan sake tsayawar gwamnan Jihar Malam Umar Dikko Raɗɗa sake komawarsa wa’adi na biyu na mulkin Jihar.

A wata hira da manema labarai da shugaban Majalisar Nasiru Yahya ya yi, ya bayyana cewa sun yanke shawarar hakan ne bayan yin dokuwar tattunawa akai.
Shugaban ya ce dukkan ‘yan Majalisar 34 sun amince da sake tsayawar Gwamna Raɗɗa a takarar gwamnan Jihar a wa’adi na biyu.

Nasiru ya kara da cewa sun gudanar da dogon bincike kan ayyukan gwamnan Radda, tare da yabawa da salon yadda ya ke gudanar da mulkin Jihar.

Shugaban ya ce gwamna Raɗɗa ya samu babbar nasarori a bangaren tsaro, noma, ilmi da tare da inganta Masana’antun Jihar.
Ya ce wadannan nasarorin ne ya sanya suka goyi bayan sake tsayawar Raɗɗa a wa’adi na biyu na mulkin Jihar.
