Akalla mutane 40 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka rasa muhallansu a rikicin ƙabilanci da ya faru a Jihar Taraba.

A wata wallafa da mai sharhi kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi Zagazola Makama ya fitar a yau Lahadi, ya ce lamarin ya faru ne makwanni biyu das suka shude.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya fara ne a ranar 9 ga watan nan da muke ciki, tsakanin wani matashi mai suna Buhari Malamby ɗan Kabilar Bandawa da kuma wasu Fulani makiyaya biyu.

Rahotannin sun kara da cewa lamarin ya samo a sali ne sakamakon shanun makiyayan sun kutsa kai cikin gonar matashin, wanda hakan ya sanya wasu matasa suka farwa fulanin da sara da adda.

A yayin rikicin Buhari Malamby ya rasa ransa, kuma hakan ya sanya ƴan Kabilar ta Bandawa suka fara yanka shanun fulanin da ke cikin daji.

Sai dai kuma hakan ya haifar da rikici, inda matasan Fulani suka isa yankin na Bandawa dauke da makamai suka hallaka matasa biyu tare da jikkata a Unguwar Munga Dasso.

Leave a Reply

%d bloggers like this: