Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa Sanata Ali Ndume ya yaba tare da jinjinawa shugaban Ƙasa Bola Tinubu bisa namijin ƙoƙarin da ya yi wajen bai’wa ƴan Arewa 12 muƙamai a cikin gwamnatinsa.

Sanata Ali Ndume ya bayyana hakan ne a jiya Asabar ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ndume ya bayyana cewa hakan babban ci gaba da ne da ya gyara rashin fahimtar da ake kallo a naɗe-naden muƙaman da shugaban Kasa Tinubu ke yi a baya.

Acewar Ndume muƙaman da shugaban Tinubu ya bai’wa ƴan Arewa hakan nuna shugaban na yin mulkinsa cikin gaskiya da adalci, ta hanyar sanya kowanne bangare a cikin harkokin gwamnatinsa.

Ndume ya kara da cewa matakin zai taimaka matuka wajen daidaita wakilci a yankin na Arewa da kuma nuna cewa yankin nada muhimmanci a cikin gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

Sanata ya ce shugaba Tinubu ya dauki matakin ne bayan jin koken al’umma, inda ya dauki matakin gyara akai.

Sannan ya ce a ko da yause shugaba Tinubu yana kokarin ganin ya gyara kuskuren da yayi a dukkan lokacin da aka sanar da shi, yana mai cewa hakan ne ke nuna alamar cewa shugaba Nagari ne.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai aka sanar da naɗin ƴan Arewan 12 a hukumomi daban-daban na Ƙasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: