Wasu yan bindiga da su ka kai hari garin Kwakas a ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Filato sun kashe wani limamin kirista da kone gidaje da dama

Lamarin ya faru jiya Lahadi da misalin karfe 9pm na dare.

An kashe Mimang Lekyil a harin da aka kai wanda ake zargi yan bindiga da kai wa.

Wannan na zuwa n bayan da yan sa kai su ka kubutar da wasu mata biyu da aka yi garkuwa da su

Wani limamin kirista Bishop Ayuba Matawal ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce an harbe lilamin kiristan ne wanda su ke zargi yan bindigan sun je ne da nufin yin garkuwa da shi.

Sai dai sun kasheshi sannan su ka yi garkuwa da mata biyu a gidan sai dai daga bisani am kubutar da su.

Gidajen da aka kone akwai na Fulani kamar yadda Saeed Adamu ya bayyana.

Zuwa yanzu yan sanda ba su ce komai a kai ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: