Rundunar yan sanda a jihar Katsina ta kama wata mata da ake zargi da hallaka kishiyarta.

Mai magana da yawun yan sanda a jihar Abubakar Sadik Aliyu ne yaa tabbatarwa da Matashiya TV hakan yau Litinin.

An kama matar mai shekaru sama da 20 da haihuwa a garin Daura da ke ƙaramar hukumar Daura a jihar Katsina.

Ya ce mijin matar mai suna Nasir Yusif ne ya sanar da su faruwar lamarin ranar Asabar da daddare.

Mijin matan ya ce bayan dawowarsa daga kasuwa ya iske uwargidan a kwance cikin jini

Bayan samun labarin hakan ne jami’an su ka yi gaggawar zuwa gidan tate da daukar matar zuwa asibiti wanda a nan aka tabbatar da mutuwarta.

Yan sanda sun kama amaryar da ake zargi mai suna Rabia Labaran mai shekaru 23 wanda ta tabbatar da zargin da ake yi mata.

Mai magana da yawun yan sanda a jihar Abubakar Sadik Aliyu yi kira ga al’umma da su guji daukar doka a hannunsu don gudun abinda ka iya zuwa ya dawo.

Leave a Reply

%d bloggers like this: