Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa ko kadan gwamnatin shi ba za ta lamunci cin zarafin yara ba a Kasar.

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a yau Talata a sakon taya murta da ya aikewa yara bisa zagayowar ranar Yara ta duniya ta shekarar 2025.

Tinubu ya ce yara su ne kashin bayan Najeriya, don haka ya zama wajibi a nema musu makoma mai kyau.

Shugaban ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da ganin ta yi aiki babu dare babu rana don ganin cewa an tabbatar da kare hakkin yara a Najeriya.

Sannan ya ce gwamnatinsa za kuma ta tabbatar da inganta rayuwar yara walwalarsu, da kuma samar musu da makoma mai kyau da hanyar ba su ilmi.

Har ila yau shugaban ya kara cewa gwamnatin tarayya da dukkannin Jihohin Najeriya 36 sun dauki da’ar kare hakkin yara daga cin zarafinsu.

Ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da ganin an kawo karshen cin zarafin yara a Najeriya, da kuma bai’wa kowanne yaro Kariya.

A kowacce ranar 27 ga watan Mayun kowacce shekara ne Majalisar dinkin duniya ta ware a matsayin ranar yara ta duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: