Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya tabbatar da cewar ba zai taɓa bari wata ƙaramar hukumar ta koma ƙarƙashin ikon Boko Haram ko ISWAP ba.

Zulum ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai bayan tattaunawa da ya yi da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu juya Litinin.

A cewar gwamnan ya je fadar shugaban kasar ne don yi wa shugaban kasa bayani dangane da sha’anin tsaro a yankin arewa maso gabas musamman jihar Borno.

A makon da ya gabata gwamnan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kai dauki kan yunkurin Boko Haram na kwace garin Marte.

A cikin ganawar da aka yi da shi ya ce kiran da ya yi ya fara haifar da da mai ido.

Sai dai ya ce a bangarensa a matsayinsa na gwamnan jihar, ba zai taɓa bari wata ƙaramar hukuma ta koma karkashin ikon yan Boko Haram ba.

Sannan yayi kira ga sojoji da sauran jami’an tsaro da su ƙara kaimi wajen ganin sun ci gaba da bai wa ƙananan hukumomin kariya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: