Tsohon gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ita ce jam’iyya mai ɗunbun tarihi da karkashin dimkradiyyar Najeriya.

Sule Lamido ya bayyana hakan ne a yau Talata a wata hira da aka yi dashi a Channels Tv.
Acewarsa babu shakka matukar jam’iyyar PDP ta rushe a Najeriya babu shakka itama Najeriya ta rushe, duba da cewa za ta faɗa hannun ƴan kama karya.

Lamido ya ce tabbas Najeriya za ta ci gaba ne matukar jam’iyyar PDP ta tsaya da kafafunta.

Har ila yau ya ce dukkan rikice-rikicen cikin gida da ake fama dashi a cikin Jam’iyyar PDP hakan ba zai karyar da gwiwarsa ya fice daga cikinta duba da muhimmancin da jam;iyyar ta ke dashi a Najeriya.