Fiye da mutane 30 yan bindiga su ka hallaka a wasu hare-hare da su ka kai jihar Benue.

Lamarin ya faru tsakanin ranakun Juma’a zuwa Lahadi makon jiya.

Shugaban ƙaramar hukumar Gwer ta arewa Ormin Torsar Victor ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai.

Ya ce an kai harin cikin ƙauyuka uku a tsakanin ranakun wanda aka kashe sama da mutane 30.

A ƙauyen Aondana mutane sama da 20 aka kashe a harin da aka kai musu ranar Lahadi, sai kuma wasu sama da kutane 10 da aka kashe a wani ƙauye.

Daga cikin waɗanda aka kashe har da yara kanana da ba su wuce shekara biyu a duniya ba

Shugaban karamar hukumar ya ce da kansa sun binne mutane biyar ciki har da wani mutum da yayansa da aka kashe a kauyen Tewa Biana kusa da sansanin sojoji.

Daga bangaren yan sanda a jihar kuwa sun tabbatar da hare-haren guda biyu, sai dai ba su ba da tabbacin mutuwar sama da mutane 20 ba.

A yan kwanakin nan dai an matsa da kai hare-hare a jihar Benue wanda hakan ke silar rasa rayuwar mutane da dama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: