Wani abu ya fashe a kusa da barikin sojoji da ke Abuja.

An j karar abin fashewar da ake zargi bam ne a kusa da Abacha Barraks da ke hanyar Nyany zuwa Maraba a Abuja yau Litinin.
Ana zargin fashewar ta jikkata mutum guda.

Wani da lamarin ya faru a gabansa ya tabbatar da cewar ya ji karar abin fashewar sai dai ba zai iya tabbatarwa da ko bam ne ya fashe ba.

Da aka ji daga yan sanda a Abuja, mai magana da yawun ƴan sanda Josephine Adeh ta tabbatar da fashewar.
Ta ce lamarin ya faru da karfe 2:50pm na rana.
Sannan ta ce su na kan bincike kan lamarin zuwa yanzu.
