Wasu da ake zargi yan bindiga ne sun kai hari wasu kauyuka a ƙaramar hukumar Munya ta jihar Neja

Yan bindigan da yawansu ya zarce 100 sun kai hari ƙauyuka uku a jiya Talata tare fa hallaka mutane da ƙone gidaje da kuma sace kayayyakin amfani ciki har da shanu sama da 200.

Ƙauyukan da aka kai harin sun haɗa da Zagzaga, Chibani da Kuchi.

Harin dai ya shafe tsawon sa’o’i uku wanda su ka bi gida gida su na sace kayayyaki

Haka zalika sun kone wani sansanin jami’an tsaron hadin gwiwa a Kuchi kamar yadda rahotanni su ka tabbatar.

Sai dai daga bisani an ga gawan dan bindiga daya.

Kwamishinan tsaro a jihar Manjo Janar Bello Abdullahi mai ritaya ya tabbatar da lamarin, sai dai ya ce ya na kan karbar bayanan yadda lamarin ya kasance.

Jihar Neja na cikin jihohin da yan bindiga su ka addaba da hare-haren tsawon lokaci, duk da kokarin da gwamnatoci ke yi na yaki da ta’addanci a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: