Tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya ce ba zai halarci taron jam’iyyar PDP ba har sai an kori ministan Abuja Nyesom Wike daga jam’iyyar.

Lamido ya bayyana haka ne bayan da ya kauracewa taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka yi jiya Talata a Abuja.


A cewarsa zaman Wike cikin jam’iyyar babbar barazana ce ga zaman lafiyar jam’iyyar da kuma samun daidaitonta
Sule Lamido ya bayyana Wike a matsayin wata annoba ga jam’iyyar wanda ya zarge shi da kokarin rusa jam’iyyar baki daya.
Lamido ya bukaci sanin dalilin da ya sa aka bar Samuel Ortom cikin kwamitin amintattu bayan da cewar ya ayyana shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda ya marawa baya.
Tsohon gwamnan Jigawan dai ya ce ya zama wajibi a kori Wike da wasu manyan jam’iyyar da ya zarga da cin dunduniyarta wanda su ke neman ganin ta rushe.