Wata babbar kotun tarayya da ke zaune a Kaduna ta ci tarar naira miliyan 900 ga tsohon gwamnan jihar Malam Nasir Elrufai.

An ci tarar Elrufai ne bayan umarnin kamawa da tsare wasu dattawa da ya sa aka yi lokacin ya na gwamna a jihar.


Mai shari’a Hauwau Buhari ce ta yanke hukuncin bayan kama wani Awemin Dio Maisamari da wasu mutane takwas kan zargin kashe wani basarake Raphael Maiwada Galadima.
Bayan binciken da kotun ta yi ta gano Elrufai na da hannu tsamo tsamo wajen sanyawa aa kama dattawan sannan a tsaresu.
Sannan kotun ta yi watsi da rokon da wadanda ake kara su ka yi wanda su ke inkarin cewar kotun ba ta da hurumin sauraron karar.
Tsohon gwamnan dai ya bayar da umarnin kama mutanen a shekaraar 2019.
Ana zargin an yi garkuwa da basaraken wanda daga bisani kuma aka kasheshi.
