Wasu da ake zargi ƴan bindiga ne sun kai hari tare da yin garkuwa da wani basarake a jihar Nassarawa.

Yan bindigan sun kai hari fadar basaraken da ke ƙaramar hukumar Kokona da daddare sannan su ka buɗe wuta.


Wani da yake a garin ya tabbatar da yin garkuwa da Mista Emmanuel Omanji a jiya Laraba da daddare.
Yan bindgan sun shiganhar fadar basaraken da ke gidansa sannan su ka tafi da shi
Jami’an yan sanda aa jihar sun tabbatar da lamarin.
A cewar mai magana da yawun yan sanda a jihar Ramhan Nansel kwamishinan yan sanda a jihar ya bayar da umarni domin haɗa tawagar jami’an yan sanda da soji don kubutar da shi
Sannan ya tabbatar da cewar za su kubutar da shi tare da bukatar bayanai daga jama’a kan lamarin.
