Jami’an tsaron Operation Hadin Kai sun kama sojoji 18 da yan sanda 15 da ke siyarwa da yan bindiga makamai.

Kwamandan rundunar Manjo Janar Abdussalam Abubakar ya bayyana haka a Maiduguri ta jihar Borno.

Ya ce an kama gurɓatattun jami’an ne a jihohin Borno ,Bauchi, Benue, Enugu, Rivers, Taraba, Kaduna, Filato, Legas Ebonyi da babban birnin tarayya Abuja.

Sanarwar da Manjo Ademola Owolana ya fitar a madadin kwamandan, ya ce an kuma kama farar hula takwas da wani basarake ɗaya.

Sannan an kama wani Ameh Raphael da ya zamto mai kula da bangaaren makamai na jami’an wanda ya fara hada hadar tun shekarar 2018 sannan an gano naira miliyan 45 a asusun ajiyarsa na banki.

Sai kuma wani Seidi Adamu da ya fara hada hadar a shekarar 2022 wanda aka gano naira miliyan 34 a asusunsa na banki.

Haka kuma akwai wani dan sanda mai suna Enoch Ngwa da aka gano naira miliyan 135 a asusunsa na banki.

Jami’an dai ana zarginsu da siyarwa da ƴan ta’adda makamaai da su ka haɗa da bindigu, harsashi da sauransu.

Idan za a iya tunawa a kwanakin baya wani bincike da aka yi aka gano batan wasu bindigu masu tarin yawa daga rundunar yan sandan Najeriya

Leave a Reply

%d bloggers like this: