Majalisar Wakilan Najeriya ta musanta batun da ake yaɗawa na cewa ana bai’wa kowane ɗan Majalisar Naira biliyan 1 a matsayin kuɗaɗan ayyukan da zai yiwa mazaɓarsa.

Kakakin Majalisar Hon Akin Rotimi ne ya musanta zargin a yau Juma’a a birnin tarayya Abuja a wani taron tattaunawa da aka shirya.
Rotimi ya ce ana yada hakan ne domin tunzura al’umma, yana mai bayyana lamarin a matsayin wanda babu gaskiya ko kadan a cikinsa.

Kakakin ya ce wanda ya fara yaɗa jita-jitar wani tsohon ɗan takarar majalisa ne, da bai samu nasara ba, kuma yayi hakan ne domin mutane su sanshi da ganin ya samu nasara a zabe mai zuwa.

Tsohon dan takarar ya ce tun bayan cire tallafin fetur da gwamnatin shugaba Tinubu ta yi ta ƙara kuɗaɗen ayyukan mazabar kowanne dan Majalisa, inda ya kara daga naira miliyan 200 zuwa naira biliyan 1 ga kowanne dan majalisar ta wakilai.
Sannan ya ce ana kuma bai’wa kowane Sanata na Majalisar Dattawa kimanin Naira biliyan biyu a matsayin suma kuɗaɗen ayyukan mazaɓa a kowace shekara.
Sai dai Rotimi ya bukaci da mutane su yi watsi da waɗannan kalamai marasa tushi.
