Wata Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta dakatar da hukuncin da wata babban kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke kan soke tsarin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Kano KASIEC, kan zaɓen ƙananan hukumomi da hukumar ta yi tun a ranar 26 ga watan Oktoba shekarar 2024 da ta gabata.

A zaman kotun na yau Juma’a, hukuncin na daga cikin hukunce-hukunce uku da kotun ta yanke.
Alƙalin Kotun Mai Shari’a Biobele Georgewill, tare da wasu alkalai biyu ne suka yanke hukuncin, inda suka ce babbar kotun ta tarayya ba ta da hurumin sauraron ƙarar da ta shafi tsare-tsaren hukumar zaɓen Kano da kuma cancantar mambobinta.

Kotun ta ce hakan ne ya sanya ta karɓi ƙarar da babban lauyan Kano, da majalisar dokokin ta Kano harma da hukumar ta KANSIEC suka shigar gabanta, sannan ta ce babbar kotun Kano ce kadai ke da hurumin sauraron ƙarar ba kotun tarayya ba.

Kotun ta kuma ce ta kori ƙarar baki daya, sakamakon cewa babbar kotun ta Tarayya ba ta da hurumin sauraron ƙarar.
A hukunci na huɗu da kotun ta yanke ranar Juma’a, ta kuma soke wani hukuncin da babbar kotun tarayya a Kano ta yanke, kan ƙin amincewa da sunayen ƴan takara daga bangaren jagoran jam’iyyar NNPP a Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya mikawa hukumar ta KASIEC kan zaɓen ƙananan hukumomin Jihar.