Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranar Juma’a da Litinin masu zuwa a matsayin ranakun hutu a fadin Kasar, don gudanar da bukukuwan babbar sallah.

Ministan Harkokin Cikin Gida Olubunmi Tunji-Ojo ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa, mai dauke da sanya hannun babban sakatariyar ma’aikatar Magdalene Ajani ta fitar a yau Litinin.
Sanarwar ta taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar, tare da yin kira garesu da su yi amfani da lokacin wajen yiwa Najeriya addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.

Sannnan sanarwar ta bukaci ‘yan Kasa da su hada kai da gwamnati domin ganin an kara daga Najaeriya a idon duniya.

Hutun zai kasance a ranar Juma’a 6 ga watan Yuni da kuma ranar Litinin 9 ga watan na Yunin da muke ciki.
