Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMet ta yi hasashen yin ruwan sama da tsawa tsawon kwana uku.

A cewarsa a hasashen da ta yi za a fara shiga yanayin ne daga yau Litinin.

A cewarta za a samu hadari da tsawa da kuma ruwan sama da safe a jihohin Taraba, Aduna, Bauchi, Kebbi, Sokoto, Katsina, Jigawa da Kano.

Sai dai ta ce za a fi samun tsawar a jihohin Kaduna, Taraba, Sokoto, Borno, Kebbi da Zamfara wanda shi ma za a fara a yau

Sannan a sassan Abuja Nassarawa da Niger ma za a samu tsawar da ruwan sama a safiyar yau.

A yammacin yau kuwa za a samu tsawar da ruwan sama a jihohin Nassarawa, Kwara, Niger, Kogi, Benue, Plateau da Abuja.

Sai kuma hadari da za a samu a jihohin Ebonyi, Abia, Rivers, Akwa Ibom, Edo, Ogun da Ondo.

A jihohin Edo, Abia, Imo, Ebonyi, Enugu, Anambra, Akwa Ibom, Cross River, Rivers, Delta, Bayelsa, Osun, Ogun, Ekiti, Ondo, Oyo da Legas za a samu ruwa sama matsakaici.

Sannan ana sa ran samun ruwan sama yau a jihohin Zamfara, Katsina, Bauchi, Adamawa, Borno, Yobe, Taraba da Kano.

Hukumar ta shawarci mutane da su kaucewa duk wata hanya da za ta iya haifar da ambaliyar ruwan sama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: