Mutane bakwai ne su ka rasa rayuwarsu sakamakon hatsarin wani kwalekwale a jihar Sokoto.

Matafiyar sun taso ne daga Gidan Hussaini zuwa Gwargawu a gundumar Kambama da ke ƙaramar hukumar Shagari a jihar
Ko da cewar ba a bayyana sunayen mutanen da su a rasu ba, sai dai wani ya tabbatar da lamarin.

Gwamnatin jihar ta aike da tawaga don jajantawa kan lamarin wanda kwamishinan kuɗi Muhammadu Jabbi Shagari wanda ya bayyana lamarin a matsayin abu mai taɓa zuciya.

Sannan ya yi wa mamatan fatan dacewar da rahamar Allah
Haka kuma ya shawarci matafiya da masu kwale kwalen da su dinga amfani da rigar kariya sannan su kaucewa lodin da ya zarce ka’ida.