Gwamnatin jihar Niger ta ce ambaliyar ruwan sama ta shafi mutane 1,354 a jihar.

Mai bai wa gwamnan shawara Murtala Bagana nr ya bayyana haka yayin da mataimakin shugaban ƙasa Sanata Kashim Shettima ya kai ziyarar jaje jihar.


A cewarsa, mutane 4,534 ne su ka rasa muhallinsu wanda ya shafi magindanta 458.
Sannan akwai gine gine gida 265 da manyan hanyoyi guda biyu sai gadoji guda biyar
Zuwa yanzu fiye da gawar mutane 200 aka gano yayin da ake ci gaba da aikin gano wasu sama da 500.
Lamarin dai ya faru a ƙaramar hukumar Mokwa a jihar wanda ya tayar da hankalin mutane da dama.
