Gamayyar Kungiyoyin Ma’aikatan Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Abuja sun bayyana shirinsu na tsunduma yajin aiki.

Ma’aikatan za su tsunduna yajin aikin ne bisa gazawa da kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja AEDC wajen cika yarjejeniyar da suka cimma tun a watan Nuwanban shekarar 2024.
Kamfanin samarwa da wuta ne a birnin tarayya Abuja, da Jihohin Nasarawa, Neja da kuma Kogi.

Gaamayyar kungiyoyin biyu sun bayyana cewa za su tsunduma yajin aikin ne ba tare da wata sanarwa ba.

Acewar kungiyoyin sun aika da takardu daban-daban zuwa ga shugaban na AEDC, kan biyansu haƙƙoƙinsu amma babu wani abu da aka yi akan lamarinsu.
Kungiyoyin sun ce sun cimma yarjejeniyar ne domin dakatar da yajin aiki da suka 27 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata.
Kungiyoyin sun ce kamfanin yaki mutunta yarjejeniyar da su cimma bisa ta rashin biyansu fansho, karin girma da kuma gaza biyan mafi karancin albashi.
A don haka Kungiyoyin suka bukaci ƴaƴansu da su kwana cikin shiri a kowanne lokaci kan tafiya yajin aikin.