A yau maniyyata su ka fita filin arfa don ci gaba da ibadar aikin hajjin bana.

Fiye da mutane miliyan ɗaya da rabi ne ke gudanar da ibadar aikin hajjin bana.

Mutane 1,673,230 ne su ka fita filin arfa a yau don ci gaba da ibadar

Musulmin sun shafe wunin yau Alhamis a filin tare da gudanar da addu’o’i da karatun Alkur’ani.
Sai dai a bana hukumomi a saudiyya sun hana mutane yin ibadar ba tare da izini ba tare da sanya tara ga dum wanda aka kama.
Daga cikin waɗanda aka saka dokar har da yan ƙasar.
Dubban mutane aka hana shiga garin Makkah don gudun rusa tsarin da su ka ɗauka a bana.
Dangane da batun yanayin zafi, hukumomi a ƙasar sun dauki matakan rage zafi kamar feshi ruwa da kuma amfani da motocin ba da agajin gaggawa don gudun jikkatar mutane.
Haka kuma maniyyatan da yawan na amfani da makarin rana wato laima wajen rage zafin a jikinsu.
Sannan an shawarci maniyyatan da su dinga yawan shan ruwa tare da zama wajen da ke da inuwa
Bayan shafe wunin yau a gobe za a fita domin sallar ido wanda daga nan za a fara jifa kuma shi ma yana daga cikin ƙaidar aikin hajjin.
Kwanaki uku ake shafewa ana yin jifan kamar yadda addinin musulunci ya kawo.