Hukumar alhazai a Najeriya ta tsayar da ranar 9 ga watan Yuni don fara jigilar dawo da alhazan Najeriya.

Shugaban hukumar Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a.

Sanarwar da ya fitar wadda a ciki ya taya al’ummar musulmi barka da sallah, ya kuma yi bayani kan ranar fara dawo da mahajjatan..
Ya ce jirgi na farko da zai fara dawo da maniyyatan shi ne Air Peace da Max Air sai Flynas.

Za a fara dawo da alhazan jihohin Imo, Bauchi Kebbi da Sokoto.

Hukumar ta NAHCON ta kuma yabawa hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi da su ka bayar da gudunmawa da jajircewarsu.

Sannan ya yabawa sauran masu ruwa da tsaki da wadanda su ka bayar da gudunmawa har aka kai matakim da ake a yanzu na samun nasarar gudanar da aikin hajjin..

Farfesa Abdallah Saleh Usman ya kuma yabawa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima da su ka yarje masa har aka samu nasarar kammala shirin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: