Uwargidan tsohon shugaban Najeriya Maryam Abacha ta musanta zarge-zargen da aka jima ana yiwa maigidan marigayi Janar Sani Abacha na yin sama da faɗi da kuɗaɗen Najeriya.

A hirar da aka yi da Maryam Abacha a ranar Lahadi a TVC, bisa cikar mijinnata shekara 27 da rasuwar.
Maryam Abacha ta tabbatar da cewa kuɗaɗen ba sace su aka yi ba, tana mai cewa mutane ne kawai suka yiwa lamarin kudeden mummunar fassara.

Idan ba a manta ba shekaru da dama da suka shuɗe gwamnatocin Najeriya daban-daban suka dawo da miliyoyin daloli wadanda aka boye su a asusun bankuna a ƙasashen ketare, da aka fi sani da kuɗaɗen Abacha.

Kuɗaɗe da aka dawo da su daga ƙasashen Switzerland, Amurka da kuma Birtaniya, an yi amfani da su wajen tabbatar da walwaka da kuma jindadin ƴan Ƙasa.
Maryam Abacha ta kuma ƙalubalanci masu zargin da su gabatar da shaida kan lamarin kudaden, inda ta ce Wanene shaida akan kuɗaɗen da aka ɓoye, kuma wa ya ga sanya hannun maigidanta akan kuɗaɗe da aka zargi an boye ketare.
Ta ce ci gaba da zargin mijinta akan lamarin hakan na nuni da matsalar da ake da ita a cikin al’umma.
Janar Sani Abacha ya mulki Najeriya a lokacin mulkin soji da kuma shugaban rundunar sojojin Najeriya tun daga shekarar 1993 zuwa 1998.
Abacha ya rasu ne a ranar 8 ga watan Yunin shekarar 1998.